Harshen yanzu: ha Halshen Hausa

Harshe
Selected Language:

Malamanmu

Da alamar gaba gaɗi da ƙauna, John Bevere shi ne marubucin da ya fi kasuwa a matsayin wanda ya yi fice, Tarkon Shaiɗan, Tsoron Ubangiji, Rufin Asiri, da kuma Izawa daga Makoma. An fassara litattafansa zuwa fiye da harsuna 100, da kuma shirinsa na gidan talabijin a kowane mako, Manzo, ana yaɗa shi a faɗin duniya. John sanannen mai wa’azi ne a taruka da ikkilisiyu, kuma ƙungiyarsa ta bishara tana rarraba kayan aiki masu canja rayuwa ga waɗanda suke son fahimta da kuma amfani da ƙa’idojin Allah. John yana jin daɗin zama a maɓuɓɓugan Colorado tare da matarsa, Lisa, wadda ita ma marubuciya ce da ake saye sosai da mai wa’azi kuma, ‘ya’yansu huɗu, sai suruka, da jikoki.

Duba abubuwan saukarwa da ke akwai Adireshin yanar gizo John Bevere

Mai kishi. Gaba gaɗi. Soyayya. Mai ƙarfi. Mai ban-dariya. Waɗannan kalmomi ne ke bayyana Lisa Bevere— The Messenger (mai wa’azi ta ƙasa da ƙasa), marubuciya da ta fi kasuwa, kuma abokiyar aiki a shirin manzo na talabijin, wanda ake yaɗawa a ƙasashe fiye da 200. A salonta na buɗe komai, Lisa tana faɗar maganar Allah da abubuwan da suka faru da ita don ta ƙarfafa jama’a su sami ‘yanci da canji. A matsayinta na ‘yar fafutukar adalci, tana jan hankalin mutane su zama amsoshi ga wasu matsaloli na matsin lamba a kusa da nesa. Tana jin daɗin ɗaukar lokaci tare da abin ƙaunarta, maigida John Bevere, da ‘ya’yansu huɗu, da suruka mai ban mamaki, da kyawawan jikoki.

Duba abubuwan saukarwa da ke akwai Adireshin yanar gizo Lisa Bevere