Harshen yanzu: ha Halshen Hausa

Harshe
Selected Language:

Shafin farko - Game da

Game da Cloud Library (ɗakin karatu na yanar gizo)

Messenger International (Manzo na ƙasa da ƙasa) ya sadaukar da kuma mayar da hankali a kan samar da kayan aiki ga Fastoci da shugabanni a faɗin duniya ba tare da la’akari da yankinsu ko kudinsu ba. An samar da Cloud Libary (ɗakin karatu na yanar gizo) don wannan manufa. Ya zama cibiya mai bada damar rarraba kayan aiki da za a iya samu a kuma saukar a sauƙaƙe.

Ƙudurinmu shi ne samar da wannan kayan aiki a cikin kowane babban harshe, da sa ran kafa matakan kaiwa ga fiye da kashi 98% na al’ummar duniya. Cloud Library (Dakin karatu na yanar gizo) na ɗaya daga cikin hanyoyin cimma wannan manufar. Me ya sa, za ka yi tambaya? Saboda kayan aiki ta yanar gizo na iya ruɓanɓanya da kuma tafiya da sauri sosai fiye da kayan aiki na zahiri. Muna fata za ka ji daɗin abin da za ka koya a cikin wannan ɗakin.

Daga masu ƙirƙirowa

Yesu bai ƙalubalance mu kan yin wa’azin bishara kawai ba, amma mu samar da almajirai. Waɗannan saƙonni za su taimake ka zama almajirin Yesu. Muna zuba jari a cikin horaswar ka saboda mun yarda da kai da kuma abin da za ka iya yi, ta wurin alherin Allah, don ka canja duniyar da kake da tasiri a kanta. Allah ya sanya iko a cikinka, kuma yana marmarin ya san ka sosai. Waɗannan kayan aiki za su taimake ka gane dangantaka ta ƙut da ƙut, tsakaninka da Allah, a yayin da kake girma cikin dangantakarka da Kiristi, ikon maganarsa zai canja ka.

Allah ya halicce ka da manufa wadda ta musamman ce ga baye-bayenka da tasirinka. Muna ƙarfafa ka ga binciken dukkan falalar da Allah ya tanadar maka. Addu’armu ita ce bari waɗannan kayan aiki su shirya ka ga tafiya zuwa ga ganewa.

Albarku a gareka kuma naka,

John da Lisa Bevere

Tallafawa Wahayin

Ko zuciyarka tana ƙuna a kan ganin cewa an rarraba waɗannan kayan aiki masu canja rayuwa a duk faɗin duniya? Idan kana da sha’awar tallafa wa aikin ɗaking karatu na yanar gizo (Cloud Library), idan ka yarda sai ka aika ta adireshin yanar gizo zuwa ga getinvolved@cloudlibrary.org. Muna gode maka tun yanzu domin addu’oi da tallafinka!